Jam´iyar adawa ta UPDS ta ƙauracewa zaɓe a Jamhuriya Demokradiyar Kongo | Labarai | DW | 02.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyar adawa ta UPDS ta ƙauracewa zaɓe a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

Yau ne hukumar zaɓe mai kanta, a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ta rufe rijistar takara, a zaɓen shugaban ƙasa,, da na yan majalisun dokoki, da za ayi a watan juni mai zuwa.

Saidai ,Ethienne Thissekedy, madugun yan adawar ƙasar bai ajje takara ba, a wannan zaɓe, kazalika, babu yan jam´iyar sa ta UPDS, ko daya da ya shiga takara, a zaɓen yan majalisun dokoki.

Tun shekara da ta gabata madugun yan adawar Jamhuriya Demokradiyar Kongo,ya bayyana ƙauracewa wannan zaɓe.

To saidai, bayan kammala zaɓen kudin tsarin mulki, ya alkawarta cewa, za ya shiga a dama da shi.

Tunni, masharahanta sun fara hasashen cewar tsugunne ba ta ƙare ba, a wannan ƙasa, dalili da ƙin shigar jam´iyar adawa a zabbukan.