Jami′an tsaro na yi wa mata fyade a Mexiko | Labarai | DW | 28.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami'an tsaro na yi wa mata fyade a Mexiko

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta Amnesty International ta zargi jami'an tsaron kasar Mexiko da yin lalata da matan da suka kama domin kwatar bayanai daga wurinsu lokacin da suka kamasu.

Amnesty International ta bayyana wannan zargi ne a cikin wani rahoto da ta fitar a wannan Talata inda ta ce sakamakon wani bincike da ta gudanar kan wasu mata 100 da ake tsare da su a gidajen kurkukun kasar ta Mexiko ya nunar da cewa 72 an ci zarafinsu ta hanyar saka musu wayoyin lantarki ko kai musu bugu a lokacin kamasu .

Rahoton ya kuma ce 70 daga cikin matan dari da aka ci zarafinsu sun shigar da kara a gaban kotu sai dai babu jami'in tsaro da ya gurfana a gaban kotun balantana a yi batun tuhuma.