1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro a kasar Jamus sun cafke wasu mutane

Zulaiha Abubakar
March 18, 2018

Jami'an tsaron Jamus sun kame mutane uku a arewacin birnin Hannover yayin da Kurdawa suke gudanar da zanga-zangar adawa da hare-haren da kasar Turkiyya ke ci gaba da kaiwa arewacin kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/2uX3q
Weitere Verhaftung eines Verdächtigen
Hoto: AP

Sanarwar ta kara da cewar sama da mutane dubu 11 ne suka gudanar da zanga-zangar tare kuma da jifan jami'an 'yan sandan Jamus da robobin ruwa da yi musu barazanar zane su da sandan tutocin da suke rike dasu yayin zanga zangar. Masu gudanar da zanga-zangar sunyi korafi akan cinikin makamai tsakanin Turkiyya da kuma kasar ta Jamus tare kuma da kiran shugaba Recep Tayyip Erdogan dan Ta'adda.

  .