1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro a Jamus sun yi nasarar dakatar da hari

Yusuf Bala Nayaya
December 23, 2016

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake cigaba da farautar dan akasar Tunisiya Anis Amri da ake zargi da kai hari a kasuwar Kirsimetin ta birnin na Berlin.

https://p.dw.com/p/2Ulvo
Deutschland Anti-Terror-Einsatz im Centro Oberhausen
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Stoffel

'Yan sanda a kasar Jamus sun sami nasara ta cafke wasu 'yan uwa guda biyu bisa zargin shiri na kai hari a wani babban rukuni na shaguna kamar yadda mahukunta suka bayyana a ranar Juma'an nan, abin da ke zuwa kawanaki hudu bayan da wani mai ikirarin Jihadi ya kutsa kai cikin wata kasuwar Kirsimeti da babbar mota ya tattake mutane da sanadi na rayukan mutane 12 a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus.

Jami'an 'yan sanda sun ce sun sami nasara ta kama mutanen biyu masu shekaru 28 da 31 wadanda 'yan asalin Kosovo ne kuma suna ci gaba da zurfafa bincike dan gano ko a kwai karin wasu mutane da ke da hannu a wannan shiri na kai hari.

Tun a yammacin jiya Alhamis aka jibge jami'an tsaro a birnin na Oberhausen na Yammacin Jamus inda rukunin wadannan shaguna kimanin 250 su ke kusa da babbar kasuwar Kirsimeti a birnin.