1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an jam'iyyar PDP a Najeriya na tattaunawa

Usman ShehuJanuary 16, 2014

Jam'iyyar PDP mai mulki ta yi na'am da takardar marabus ɗin shugabanta Alhaji Bamanga Tukur a ƙarshen wani taronta.

https://p.dw.com/p/1AsPM
Nigeria Abuja PDP Bamanga Tukur
Hoto: Philip Ojisua/AFP/Getty Images

Cikin ƙasa da tsawon mintuna biyar ne dai aka kawo ƙarshen taƙaddamar da ta ɗauki wata da watanni sannan kuma ta yi barazanar kawo ƙarshen tasirin jam'iyyar PDP mai mulki a cikin Tarrayar Najeriya na lokaci mai tsawo. Babu dai ɓata lokaci a ɓangaren mahalarta taron da suka ce sun karɓi ajiye aikin shugaban sun kuma amince da ƙoƙarin sake naɗin wani shugaban cikin tsawon kwanaki huɗu masu zuwa .

Matamaikin shugaban jam'iyyar shi ne zai yi riƙon ƙwarya kafin naɗa sabon shugaba

A yau jam'iyyar da rashin shugaban jam'iyyar,mataimakin shugaban jam'iyyar zai ɗau ragamarta har na tsawon wasu kwanaki huɗu. Ranar Litinin 20 ga watan Janairu dai kwamitin zartarwa jam'iyyar zai sake taruwa domin zaɓen sabon shugaba kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanadar. Saukar ta Bamanga dai ta ɗauki lokaci yana ja da ikon gwamnonin cikin jam'iyyar masu ƙarfin tasiri da ya kama hanyar buɗe sabon babi a cikin jam'iyyar. Wani rikicin cikin gidan na jam'iyyar shi ne na jihar Adamawa a fito na fito da ake yi tsakanin ɓangarori daban-daban na jam'iyyar da ta fuskanci barazana mafi tasiri a cikin tarihinta na shekaru16.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Saukar ta Bamanga za ta taimaka ga warware rikicin jam'iyyar

Abun kuma da ya ɗan kwantar da hankula a tsakanin masu ruwa da tsakin PDP da ke kallon sabon matakin a matsayin kama hanyar kawo ƙarshen rikicin a faɗar Auwalu Audu Gwalabe da ke zaman mataimakin ma'ajin kuɗi na jam'iyyar na kasa wanda ya ce ana daf da samun msalha. Ya zuwa yanzu dai 'yan takara kusan tara ne ake batu tsakanin sabbabi jinin dama wanda jinin nasu ya fara nuna alamun tsinkewa daga yankin na arewa maso gabas, ke neman gadon kujerar da ake yi wa kallon mai tasiri a cikin PDP da ke ƙara kusantar zaɓukan Tarraya a baɗi. To sai dai kuma na kan gaba a ciki na zaman Mohammed Wakil da ke zaman tsohon shugaban masu rinjayen majalisar wakilan ƙasar daga Borno da kuma ke samun ɗaurin gindin shugaban ƙasar da mataimakinsa, da kuma Abdullahi Mai Birgi a Adamawa da shi kuma ke da goyon bayan su Jerry gana da Edwin clark, sannan kuma da Aliyu Habu fari a jihar Tarraba game kuma da Abdullahi Idris da ke zaman ministan sufurin ƙasar daga Gombe. Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabon sauyin ga makomar PDP dama fatan sake ci gaba da babakerenta cikin harkokin siyasar ƙasar na lokaci mai tsawo.

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf
Hoto: DW/U.Haussa

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da hirar da Salissou Boukari ya yi da Farfesa Kamilu sani Fagge masanin kimiyar siyasa, kuma malami a jami'ar Bayero da ke Kano a kan wannan batu

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani