Jami′an diplomasiya sun damu da halin da ake ciki a Burundi | Labarai | DW | 12.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami'an diplomasiya sun damu da halin da ake ciki a Burundi

Burundi tana kara fuskantar matsalolin siyasa tun bayan da shugaban kasar ya yi tazarce, abin da nema sake jefa kasar cikin yakin basasa

Jami'an diplomasiya sun yi gargadi kan yadda gwamnatin kasar Burundi ta fara watsi da shirin raba madafun iko tsakanin kabilun kasar, abin da ke zama daya daga cikin jiga-jigan matakin yarjejeniyar zaman lafiya da ta kawo karshen yakin basasan kasar na tsawon shekaru 13.

Jami'an na diplomasiya daga Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar Tarayyar Afirka, da Tarayyar Turai, gami da Amirka sun bukaci bangarorin da ke rikici da juna kan tattaunawa da samun mafita ta siyasa. Kuma sun fadi haka cikin wata sanarwar da suka fiyar. Tun cikin watan Afrilu kasar ta Burundi ta fara shiga rikicin siyasa lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyar sake takara a karo na uku, inda daga bisani ya lashe zaben da aka shirya mai cike da rudani.

Wani kiyasi Majalisar Dinkin Diniya ya nuna fiye da mutane 180,000 suka tsere daga Burundi, domin tsoron tashin hankali, inda ake sa ran adadin zai karu. Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin dan Adam ya ce al'amura suna kara sukurkucewa a kasar ta Burundi, sakamakon hare-hare da ake kai wa musamman kan wadanda suka yi adawa da tazarcen Shugaba Nkurunziza.