Jamhuriyar Nijar: Harin ta′addanci ya halaka soji 16 | Labarai | DW | 03.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamhuriyar Nijar: Harin ta'addanci ya halaka soji 16

Kimanin jami'an sojojin Jamhuriyyar Nijar 16 ne suka gamu da ajalinsu yayin da soja daya ya bace, bayan wani hari da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai musu a inda suke ran gadi a yankin Tahoua.

A cewar sanarwar da sakataren tsaron yankin Ibrahim Miko ya yi wa gidan talabijin da maraicen jiya.

Daga cikin wadanda ajalin nasu ya sauka harda laftanar Mamman Manewa da ke zama kwamandan rundunar. Ire-iren wadannan hare-haren dai an jima ana aiwatar da su, ko a watan Maris din da ya gabata a wannan yankin da ke makwabtaka da Kasar Mali da Burkina Faso an kai wa wasu kauyuka uku hari da kuma ya yi sanadiyar rayuka sama da mutum 140. harin da ke zama mafi muni da ya auku a kasar.

Tun a shekarar 2012 ayyukan ta'addanci ke aukuwa a wannan yankin da ma kasashen da ke makwabtaka da shi.

A baya dai kungiyoyin da ke mubaya'a da Al-Qaeda da kuma IS sun sha daukar alhakin hare-haren da ya gudana, sai dai ya zuwa yanzu babu wata kugiya da ta dauki alhakin wannan da ke zama na baya-baya.