Jamhuriyar Nijar: Cece kuce kan harkokin siyasa | Siyasa | DW | 17.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamhuriyar Nijar: Cece kuce kan harkokin siyasa

Yayin da aka shirya gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, har yanzu akwai sabani tsakanin 'yan siyasar kasar ta Nijar.

A jamhuriyar Nijar harkokin siyasar kasar na tafiya ba tare da jagoran 'yan adawar kasar kuma shugaban jam'iyyar Lumana Afrika, Mallam Hama Amadou ba, wanda aka garzaya da shi wani asibitin kasar Faransa sakamakon rashin lafiyar da yake fama da shi. Da ma Hama Amadou na gidan kaso a Nijar saboda zargin hannu a badakalar cinikin jarirai, zargin da 'yan adawa suka ce siyasa ce kawai.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin