Jamhuriyar Benin: Zaben majalisar dokoki | Labarai | DW | 28.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamhuriyar Benin: Zaben majalisar dokoki

A wannan Lahadin ne al'ummar jamhuriyar Benin ke gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki inda duka 'yan takarar suka kasance na bangaren gwamnatin mai ci ba tare da 'yan takara daga bangaren adawa ba.

Hukumar zabe mai zaman kanta ce ta hana sauran jam'iyyun biyar shiga zaben, bayan da ta ce 'yan takarar ba su cika takardu kamar yadda dokar kasa ta tanadar ba da kuma laifuka na rashin biyan haraji. Matakin hukumar zaben ya janyo mata suka daga sassa daban-daban. Ana zargin gwamnatin Shugaba Patrice Talon da yin katsalandan cikin harkokin zaben kasar.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta nuna damuwa kan yadda ake tauye hakkin dan adam a jamhuriyar ta Benin, kama daga hana 'yan fafutuka da 'yan jarida 'yancin walwala, da kuma matakin amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati.