Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya: Musulmi na barin addininsu | Labarai | DW | 31.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya: Musulmi na barin addininsu

Wani matashi Musulmi dan shekaru 23 ya fada wa kungiyar ta Amnesty cewa an tilasta masa shiga darikar Katolika ko kuma a kashe shi.

Zentralafrikanische Republik Seleka Rebellen

'Yan tawayen Seleka

Kungiyar kare hakin bil'Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa al'ummar Musulmi na fiskantar barazana a bangarori da ke a Yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda ake tilasta wa mutane na boye addininsu na Musulinci ko kuma su shiga addinin Kirista saboda barazanar kisa.

A cewar kungiyar ta Amnesty a rahoton da ta fitar a ranar Juma'an nan, wannan tilastawa ba ta shafar yankunan da dakarun wanzar da zaman lafiya daga Majalisar Dinkin Duniya ke sanya idanu a kasar.

Wani matashi dan shekaru 23 ya fada wa kungiyar ta Amnesty cewa an tilasta masa shiga darikar Katolika ko kuma a kashe shi.

Wannan kasa dai ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fada rikici mai nasaba da addini tun a shekarar 2013, lokacin da 'yan Seleka da ke zama mafi akasari Musulmi suka karbi mulki kuma yadda suka rika kama karya, ya sanya an sami kungiyoyi da dama na mabiya addinin Kirista suka tashi tsaye da kai farmaki ga mabiya addinin na Islama.