Jama′a na cikin wahala a yanki arewacin Mali | Labarai | DW | 08.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jama'a na cikin wahala a yanki arewacin Mali

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce rashin tsaro da ake fama da shi a arewacin Mali haɗe da ƙarancin cimmaka ya saka wasu jama'ar dubu 500, cikin wani hali na rashin tabbas

Militiaman from the Ansar Dine Islamic group, who said they come from Niger and Mauritania, ride on a vehicle at Kidal in northeastern Mali in this June 16, 2012 file photograph. To match Special Report MALI-CRISIS/CRIME REUTERS/Adama Diarra/Files (MALI - Tags: CIVIL UNREST CRIME LAW POLITICS)

Ansar Dine Kämpfer in Mali

Shugaban ƙungiyar Peter Maurer ya ce tun bayan da ƙasar ta rabu gida biyu a cikin watan Maris da ya gabata ;ayyukan jin ƙaI da suke yi, suka ja da baya ,saboda wahalolin da suke gamuwa da su a yankin na arewaci.

Ya ce mutanen,na buƙatar agaji saboda su ka ɗai karan kansu, ba zasu iya ɗaukar nauyin ɗawainiyar su ba.Nan gaba ne kuma a ranar lahadi mai zuwa aka shirya shugabannin ƙungiyar ƙasashen yammancin Afirka na ECOWAS ,zasu gudanar da wani taro a birnin Abuja na Tarrayar Najeriya domin tantance matakai na ƙarshe a kan yan tawayen na Mali gabannin samun izinin fara kai harin daga MDD.

A ranar talata da ta gabata ne ,man'yan kwamandojin yaƙi na ƙungiyar ƙasashen yammancin Afirka wato ECOWAS ko kuma CEDEAO;suka amince da wani tsari na sake ƙwato yankin arewacin ƙasar Mali ,wanda ke cikin hannu ƙungiyoyin yan tawayen tun watanni takwas da suka wuce .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu