Jama′a na cikin murna a Timbuktu | Labarai | DW | 29.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jama'a na cikin murna a Timbuktu

Murna ta kaure dangane da yadda sojojin Faransa da na ƙasashen Afirka da ke tallafa wa sojojin Mali suka sake ƙwacce birnin daga cikin hannun masu kishin addini.

Rahotanni daga birnin Timbuktu na cewar jama'a na ci gaba da kasancewa cikin farin ciki, bayan da sojojin Faransa da ke dafa wa dakarun Mali suka sake ƙwato birnin daga hannun masu kishin addini waɗanda suke riƙe da shi kusan watanni da dama.

A lokacin da sojojin na Faransa da na Mali da kuma na Tarrayar Afirka ke tinkarar garin na Timbuktu ɗaruruwan jama'a ne suka yi lale marhabin da su, inda wani mazaunin garin ya ke cewar a da, suna cikin tsoro da fargaba, ba su samun yin barci, amma yanzu ya ce sun samu kan su. Masu kishin addinin gabannin ficewar su ,daga birnin sai da suka ƙwana duban littattafai na tarihi a gidan adana kayan tarihi na garin.Yanzu haka kuma a kwai rahotannin da ke cewar 'yan tawayen sun sulale cikin jama'ar birnin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh