Jama′a a Najeriya na yi wa harkokin tsaro sako-sako | Siyasa | DW | 02.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jama'a a Najeriya na yi wa harkokin tsaro sako-sako

Masana harkokin tsaro a Najeriya dai sun yi gargadi kan rikon sakainar kashi da jama'a ke yi wa lamuran tsaro a kasar.

Masana tsaro a tarayyar ta Najeriya sun yi kashedi ga jama'a kan yadda suke yi wa lamuran tsaron rikon sakainar kashi saboda tunanin an kawo karshen hare-hare kungiyar Boko Haram inda aka fara yin watsi da matakan tsaro na kare kai da jama'a ke yi.

Yanzu haka dai jama'a sun yi watsi da bincike da ake yi wa mutane da suke shiga kasuwanni da tashoshin motoci da wuraren ibada a jihohin Arewa maso Gabashin kasar saboda yadda aka dauki lokaci ba a samu hare-haren bam a wasu wuraren ba.

A ziyarar da wakilinmu na Gombe Al-Amin Suleiman Mohammad ya kai wasu wuraren taruwar jama'a da suka hada da kasuwanni da tashoshin motoci da wuraren wasanni da ma wuraren ibada a birnin Gombe ya tarar da cewa an rage binciken kwakwab da ake yi wa jama'a inda a wasu wuraren ma an daina binciken kwata kwata.

Sako-sako ga lamuran tsaro

Haka wannan yanayi yake a sauran jihohin shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya ba kamar watannin baya ba da hare-haren bama-bamai na kunar bakin wake suka tsananta.

Selbstmordanschlag in Maiduguri, Nigeria

Sojoji kadai ba za su iya tabbatar da tsaro ba

Wannan ya sa masana tsaro yin gargadi ga jama'a don ganin har yanzu ba a kai ga karshen matsalar tsaron ba musamman ganin yadda ake ci gaba da samun hare-haren kunar bakin wake a jihohin Borno da Yobe.

Malam Ibrahim Baffa wanda aka fi sani da Kawu wani mai fashin baki ne kan harkokin tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya wanda ya ce jama'a sun fara yin sakaci ga batun a tsaro.

A cewar masana tsaro dai yin saken da jama'a ke yi yana da matukar hadari kamata ya yi a ci gaba da yin binciken tun da ana samun sakamako mai kyau saboda tabbatar da tsaro ba wai kawai na hukumomi ba ne, jama'a ma za su ba da ta su gudunmowar.

Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari

Kyakkyawan fata cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai magance matsalar tsaro

Alhaji Muhammad Kabir Magaji shugaban kungiyar direbobi ta Employer reshen jihar Gombe na ganin kyakkyawan fata da jama'a ke da shi kan wannan sabuwar gwamnatin ne ya haifar da wannan yanayi sai dai ya shawarci jama'a da su ba da ta su gudunmowa don kare rayukan al'umma.

Rigakafi ya fi magani

Sai dai duk da wannan gargadi da dama fargaba da masana tsaron ke bayyanawa al'ummar yankin sun yi imanin cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai magance matsalar rashin tsaron saboda kwarewarsa da kuma yadda ya san shiyyar Arewa maso Gabashin kasar.

To sai dai duk da wannan kwarin guiwa da jama'a ke da shi masana tsaron na jaddada matsayinsu na jama'a su yi takatsantsan don a cewar su aikin tabbatar da tsaro ba na gwamnati ita kadai ba ce.

Sauti da bidiyo akan labarin