Jakay Kikwete ya lashe zaben shugaban kasar Tanzania | Labarai | DW | 18.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jakay Kikwete ya lashe zaben shugaban kasar Tanzania

Ministan harkokin wajen Tanzaniya Jakay Kikwete zai kasance sabon shugaban kasar dake yankin gabashin Afirka. Sakamakon karshe da hukumar zaben kasar ta bayar yau lahadi na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar laraba ya nunar da cewa Kikwete ya samu kashi 85 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada. Hakan dai zai ba Kikwete mai shekaru 55 da haihuwa damar maye gurbin shugaba mai ci Benjamin Mkapa wanda bai tsaya takara ba bayan cikar wa´adin mulkin sa har sau biyu. A cikin yakin neman zaben mista Kikwete ya ce ci-gaba da aiwatar da manufofin sakarwa harkokin kasuwanci mara kamar yadda magabacinsa ya faro.