Jakadan MDD kan rikicin Siriya zai yi murabus | Labarai | DW | 17.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jakadan MDD kan rikicin Siriya zai yi murabus

Jakadan musamman daga Majalisar Dinkin Duniya don sulhunta rikicin Siriya Staffan de Mistura ya bayyana cewa zai ajiye mukaminsa bayan sama da shekara hudu yana wannan mukami.

Jami'in diflomasiyar wanda shekarunsa 71 a duniya zai ajiye mukamin ne a wata mai zuwa kamar yadda ya fada wa kwamitin sulhun Majaliar Dinkin Duniya a birnin New York.

De Mistura ya ce wannan ajiye mukamin nasa ya yi shi ne don wasu dalilai da suka shafe shi. Ya dai ba da muhimmiyar gudunmawa a kokarin ganin bangarorin da ke fada da juna a rikicin na Siriya da ya faro a shekarar 2011 sun koma kan teburi don warware matsalar da har kawo yanzu ta gagara. 

De Mistura ya ce zai yi amfani da makon da ya saura a wannan aiki wajen ganin an samar da kwamitin da zai yi aiki wajen ganin an samar da sabon kundin tsarin mulki ga kasar Siriya.