Jakadan EU a Tukiryya ya yi marabus | Labarai | DW | 14.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jakadan EU a Tukiryya ya yi marabus

Hansjörg Haber ya yi marabus ba tare da bayyana dalilai ba,Sai dai a can baya ya sha yin kakkausar suka a kan Turkiyya a game da yadda take wa matakan yarjejiyar da aka cimma tsakaninta da EU rikon sakainar kashi.

Jami'in na diplomasiyar wanda dan asilin Jamus ne bai ba da karin bayyani ba a game da ajiye aikin nasa.Sai dai a can baya ya sha yin kakkausar suka a kan Turkiyya a game da yadda take wa matakan yarjejiyar da aka cimma tsakaninta da Kungiyar Tarrayar Turai rikon sakainar kashi musammun ma kan tudadar yan gudun hijira zuwa nahiyar Turai.

Haka shi ma kwamitin na EU bai bayar da wani karin haske ba a kan marabus din na Hansjörg.A tsakiyyar watan Mayun da ya gabata ne aka nadashi a matsayin jakadin na EU a Turkiyya kuma zai ajiye mukamin ne a cikin watan Augustan da ke tafe.