1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya ta sake mayar da jakada Faransa

Suleiman Babayo AH
January 5, 2022

Shugaba Abdelmadjid Tebboune na kasar Aljeriya ya ba da umurni ga jadakan kasar da ke Faransa ya sake komawa bakin aiki.

https://p.dw.com/p/45BvD
Algerien | Präsident Abdelmadjid Tebboune
Hoto: Billal Bensalem/NurPhoto/picture alliance

Jakadan kasar Aljeriya da ke Faransa ya koma bakin aiki bayan janye shi tun watan Okotoba da mahukuntan Aljeriya suka yi, domin nuna takaici bisa kalaman Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da suke ganin cin fuska ne ga kasar ta Aljeriya.

Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya gana da jakadan Mohamed Antar-Daoud tare da ba shi umurnin komawa bakin aiki a birnin Paris na Faransa. Ana samun tsamin dangantaka a wasu lokuta tsakanin kasashen na Faransa da Aljeriya. Ita Faransa ce ta yi wa Aljeriya mulki mallaka inda ta shafe fiye da shekaru 130 tana karkashin kasar ta Faransa kafin samun 'yanci a shekarar 1962, kimanin shekaru 60 da suka gabata.