Jagoran ′yan adawa a Zimbabuwe na cikin mawuyacin hali | Labarai | DW | 06.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran 'yan adawa a Zimbabuwe na cikin mawuyacin hali

Jagoran 'yan adawa kuma mai neman kujerar shugabancin kasar Zimbabuwe Morgan Tsvangirai na cikin matsanancin hali sakamakon fama da cutar sankara tun shekaru biyun da suka gabata.

Simbabwe Morgan Tsvangirai in Harare Krankenhaus (AP)

Wani jigo a jam'iyar MDC mai dawa ya shaida wa magoya baya a wannan Talata cewar duba da rahoton da likitoci su ka bayar akan yanayin da Tsvangirai ya ke ciki ya na shawartar magoya baya da su shirya karbar duk abinda ya biyo baya

Wannan lalura da ta kwantar da 'dan gwagwamayar ta janyo rarrabuwar kai a cikin 'jan iyar sa ta MDC in da manyan 'yan jam'iyyar su ka mayar da hankali wajen wa zai gaje shi.Tun a watan da ya gabata Tsvangirai ya shaidawa manema labarai cewar lokaci ya yi da masu yawan shekaru ya kamata su ja baya su ba matasa guri don shugabancin kasa.

A daya bangaren shugaban kasar Emmerson Mnangagwa na ci gaba da hangen nasara a zaben kasar mai zuwa a watannin shida.