Jagoran Hamas ya koma gida Gaza | Labarai | DW | 07.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran Hamas ya koma gida Gaza

Khaled Meshaal ya kwashe shekaru 45 ya na gudun hijira a cikin ƙasahen Masar da Siriya da kuma Qatar

Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service A Palestinian man hangs a poster depicting Hamas chief Khaled Meshaal in Rafah, in the southern Gaza Strip December 6, 2012. Meshaal will make his first visit to the Gaza Strip on Friday to attend the Palestinian Islamist group's 25th anniversary rally, Hamas sources said on Wednesday. The two-day visit comes in the wake of last month's air offensive by Israel against Hamas and other armed Islamist factions to stop them firing rockets from the enclave at southern Israeli towns. REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa (GAZA - Tags: POLITICS)

Chalid Maschal in Gaza

Jagoran ƙungiyar ya ce a shirye ya ke ya mutu a Gaza inda ya ke fatan ya yi shahada.Meshaal wanda ke yin magana a birnin Gaza inda ya yadda zango a karon fako cikin shekaru 45 ya samu tarbe daga hukumomin ƙungiyar ta Hamas mai fafutukar samar da yanci falasɗiniyawa.

An tsara zai halarci wani babban gangami a gobe asabar na nuna murna samu nasara da ƙungiyar Hamas ta yi akan Isra'ila a gwabzawar da suka yi ta baya baya nan a cikin watan jiya.Ɗan gwagwarmayar , ya bar yanki yammancin gokin Jodan inda ya ke da zama , tun ya na da shekaru 11 zuwa Masar kafin daga can ya zarce zuwa Siriya kana daga bisani ya koma a Qatar.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh