Jagoran dakarun kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya ajiye aiki | Labarai | DW | 12.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran dakarun kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya ajiye aiki

Sakatare Janar na Majalisar Dikin duniya ya ce jagoran dakarun kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya ajiye aiki

Jagoran dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Babacar Gaye dan kasar Senegal ya ajiye aiki, bayan zargin dakarun da lalata da kananan yara.

Sakatare Janar na majalisar Ban ki-moon ya shaida wa manema labarai cewa ya amince da murabus da Gaye dan shekaru 64 ya yi. Tun Ban ya nuna takaici bayan bankado abin kunya na lalata da kananan yara. Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi kasashen da suke ba da dakarun kiyaye zaman lafiya su yi bincike tare da hukunta sojojinsu da aka samu da laifi.