Jagoran adawa ya lashe zabe a Kwango | Labarai | DW | 10.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran adawa ya lashe zabe a Kwango

Sakamakon zaben kasar dai da aka yi ranar 30 ga watan Disamba ya zo da ba zata inda ake tsammanin Emmanuel Ramazani Shadary da ke samun goyon baya na Joseph Kabila zai lashe shi ganin yadda yake zama na kusa da shugaban.

Jagoran adawa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Felix Tshisekedi ya lashe zaben da aka yi kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta a kasar ta bayyana a ranar Alhamis. Zaben da ya kafa tarihi a wannan kasa inda wata gwamnatin farar hula za ta mika mulki a hannun wata ta farar hula.

Sakamakon zaben kasar dai da aka yi ranar 30 ga watan Disamba ya zo da ba zata inda ake tsammanin Emmanuel Ramazani Shadary da ke samun goyon baya na shugaban kasa Joseph Kabila zai lashe shi ganin yadda yake zama na kusa da shugaban.

Tshisekedi, dan shekaru 55 ya samu kuri'u miliyan bakwai yayin da Shadary ya samu sama da miliyan hudu da Martin Fayulu shima da ke zama dan adawa ya samu sama da miliyan shida.