Jagoran adawa ya gargadi sojojin Venezuela | Labarai | DW | 11.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran adawa ya gargadi sojojin Venezuela

Wannan gargadi dai na Guaido na zuwa yayin da kungiyoyi na agaji suka dau harama tare da sa idanu kan wa ke da karfin fada aji tsakanin Guaido da Shugaba Nicolas Maduro su kuma sojoji na tsakiya.

Jagoran  adawa a kasar Venezuela Juan Guaido da ya samu goyon baya na kasashe kimanin 50 a matsayin shugaba na riko a kasar ya yi gargadi ga sojojin na Venezuela da cewa matakin da suka dauka na hana shiga da kayan agaji kasar "laifi ne na take hakkin bil Adama."

Wannan gargadi dai na Guaido na zuwa yayin da kungiyoyi na agaji suka dau harama tare da sa idanu kan wa ke da karfin fada aji tsakanin Guaido da Shugaba Nicolas Maduro su kuma sojoji na a tsakiya.

Kwanaki uku kenan da magunguna da kayan abinci na Amirka aka dakatar da su a garin Cucuta na Kwalambiya da ya raba iyaka tsakanin Kwalambiya da Venezuela. Daga bangaren na Venezuela likitoci da jami'an lafiya da dama sun gudanar da zanga-zanga inda suka nemi Shugaba Maduro ya ba da dama a shigo da kayan tallafin saboda halin da al'umma ke ciki.