1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jadawalin Mo Ibrahim ya hangi nasara

Suleiman Babayo YB
October 29, 2018

Duk da irin nasarorin akwai matsala musamman ta fannin ilmi. Mauritius ta kasance kan gaba wajen bunkasa a fannin na ilmi yayin da kasar Somaliya ke matsayi na karshe a nahiyar.

https://p.dw.com/p/37KbV
Mo-Ibrahim-Index für Regierungsführung in Afrika, 29.09.2014 in London
Hoto: Barefoot Live

A wannan Litinin aka saki rahoton shekara-shekara na gidauniyar Mo Ibrahim bisa harkokin gwamnati a kasashen nahiyar Afirka a birnin London na kasar Birtaniya, inda aka gano cewa abubuwa suna inganta sannu a hankali cikin kasashen, duk da haka ba a samu gagarumin ci-gaba da ake bukata ba, musamman duba da faduwar darajar ilimi a shekaru 10 da suka gabata.

Rahoton na shekara ta 2018 kan kasashen 54 na nahiyar Afirka, abin da aka mayar da hankali sun hada da tsarin rayuwa, da bin doka da oda, da shigar mutane a dama da su kan harkokin gwamnati da rayuwa, da kare hakkin dan Adam gami da samar da tattalin arziki bisa tsarin ci-gaba mai dorewa da bunkasar al'umma.

Mauritius Vertribenne von den Chagos Inseln oder British Indian Ocean Territory
Al'umma a wani yanki na Mauritius Hoto: imago/Le Pictorium

Gidauniyar ta Mo Ibrahim daya daga cikin shahararrun masu arziki na Afirka ya duba gwamnati ta fannin siyasa da tsarin rayuwar yau da kullum da kuma tattalin arziki ga al'umma. Yannick Vuylsteke ke jagorancin bincike na gidauniyar: "Galibi labarin maras dadi ya fi saurin tafiya cikin rahotanni, amma akwai kyawawan sakamako da aka samu. Mun ga nasarori wajen gina kayayyakin more rayuwa da cike gibi tsakanin maza da mata da ke kara karfafa. Labari mafi zama na ci-gaba na bangaren kula da kiwon lafiya. Wannan na karfafa ci-gaba bisa harkokin gwamnati a kasashen da dama."

Tsarin kiwon lafiya na daga cikin abubuwa da nahiyar ta Afirka ta samu gagarumin bunkasa cikin 'yan shekarun da suka gabata kamar yadda jami'in Yannick Vuylsteke ya yi karin haske: "Fiye da kashi 90 cikin 100 na mutane sun samu bunkasa bisa inganta lafiya. An samu rage mutuwar kananan yara da maganin cutar AIDS a kusan daukacin kowace kasa da ke nahiyar a shekaru 10 da suka gabata."

Duk da irin nasarorin akwai matsala musamman ta fannin ilmi. Mauritius ta kasance kan gaba wajen bunkasa a fannin na ilmi yayin da kasar Somaliya ke matsayi na karshe a nahiyar da aka samu bunkasa mutane da kashi 26 cikin 100 a shekaru 10 da suka shude, sannan kashi 60 cikin 100 a shekaru 25 da suka gabata, inda yawan mutane ya haura tsarin ilimin kasashen.

Somalia Mogadishu Autobombe
Rashin tsaro na zama a gaba wajen dagula lamura a SomaliyaHoto: Reuters/F. Omar

Rahoton na Gidauniyar Mo Ibrahim ya nuna cewa a shekara ta 2017 kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, da Equatorial Guinea gami da Libiya sun samu maki mafi karanci kan inganta harkokin gwamnati. Yayin da kasar Cote d'ivoire ta kasance inda ake samun ci-gaba da kowane fanni da aka gwada mizanin nasarorin da aka samu. A daya bangaren kasar Tunisiya ta gaza ci gaba da dorewar nasarori kare hakkin dan Adam da damawa da mutane a harkokin gwamnati, ita kuwa Habasha ta samu koma-baya kan bunkasa ta tattalin arziki.