1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jacob Zuma zai gurfana a gaban kotu

Yusuf Bala Nayaya
March 26, 2018

Hukumar da ke shigar da kara a Afirka ta Kudu ta bayyana a farkon wannan wata cewa za ta gurfanar da Zuma kan tuhuma goma sha shida.

https://p.dw.com/p/2v1kv
Südafrika Jacob Zuma
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/A. Ufumeli

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma zai bayyana a gaban kotu ranar shida ga watan Afrilu don ya fiskanci tuhuma da a ke masa ta wakaci ka tashi da kudi sama da dala miliyan dubu biyu na kudin makamai kamar yadda lauyansa ya bayyana a wannan rana ta Litinin.

Hukumar da ke shigar da kara a Afirka ta Kudu ta bayyana a farkon wannan wata cewa za ta gurfanar da Zuma kan tuhuma goma sha shida a badakalar da ta shafi cin hanci da rashawa da karkatar da kudin al'ummar kasa da sauransu. Wannan dai ana masa wani kallo na ci gaba a nahiyar da ba kasafai a ke gurfanar da shugabanni ba a kotu.