Jacob Zuma yayi Tazarce a shugabancin jam′iyar ANC | Siyasa | DW | 18.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jacob Zuma yayi Tazarce a shugabancin jam'iyar ANC

Wakilai a babban taro na 53 na jam'iyar dake mulki a Afirka Ta Kudu ta ANC sun zabi shugaba Jacob Zuma a matsayin shugaban jam'iyar.

Matakin da wakilan suka dauka, ya zo ne a daidai lokacin da jam'iyar take fama da gwagwarmayar neman madafun iko tsakanin Bangarorinta daban daban da kuma zargin cin rashawa a cikinta. Bisa al'ada, shugaban jam'iyar ta ANC shine kuma zai zama dan takararta a zaben shugaban kasa na gaba a shekara ta 2014.

Ku bari mu rage tazarar dake akwai tsakanin shugabanni da sauran wakilai a jam'iyarmu. Wadannan dai sune kalmomin da shugaban Afirka ta kudu, Jacob Zuma ya fara amfani dasu, a jawabinsa na bude babban taro na 53 na jam'iyar dake mulki ta ANC gaban wakilai kimanin 4000. Mahalarta taron kuwa sun amsa kiran da yayi, inda suka dorawa masa nauyin aiwatar da wannan gagarumin aiki na hade kan jam'iyar. A kuri'ar da aka kada daga baya, wakilai 2978 ne suka goyi bayan ci gaba da kasancewar Zuma kan mukamin shugaban jam'iya, yayin da abokin adawarsa, kuma tsohon mataimakinsa, Kgalema Motlanthe ya tashi da kuri'u 991. Hakan dai ya sanya kyautata zaton cewar Jacob Zuman ne zai zama dan takarar jam'iyar ta ANC a zaben shugaban kasa na gaba na shekara ta 2014.

Wiederwahl Präsident Jacob Zuma ANC Südafrika Afrika

Shugaban kasa Jacob Zuma(hagu) da mataimakinsa, Kgalema Motlanthe

Duk da gwagwarmaya a yan watannin baya tsakanin bangarori dabam dabam da yunkurin yiwa shugaban juyin mulki a jam'iyar, sake zabensa kan shugabancin ANC bai zama abin mamaki ba. Rassan jam'iyar da kuma kungiyoyin mata da na matasa da suke masu karfin fadi aji ne a cikinta tun da farko sai da suka baiyana cikakken goyon bayada biyayyarsu a gareshi. Sakatare janar Gwede Mantashe yace ko da shike ANC karuwar jam'iya ce amma kungiyoyin cikinta da basa ga-maciji da juna suna rage karfinta na na aiwatar da bukatun da ta sanya a gaba.

Lokacin da aka kammala kidaya kuri'un da aka kada na zaben shugaban jam'iyar ta ANC ranar Talata, darektan cibiyar nazarin harkokin democradiya a jami'ar Johannesburg, Steven Friedman yayi sharhi da cewa:

"Yana da kyau ganin yanzu tare da babban rinjaye an zabi shugabanninta. To amma hakan ba yana nufin an kusanci samun nasarar shawo kan matsalolin dake ci gaba da hana ruwa gudu bane a jam'iyar ta ANC, abin da shi kansa shugaba Zuma ya nunar a jawabinsa gaban taron. A gani na, abu mafi kyau shine ANC ta nemi hanyoyin shawo kan matsalolin da take fama dasu amma ba ta nemi kauce masu ba."

A jawabinsa na bude taron tun a ranar Lahadi, Zuma yayi kokarin kwantar da zukatan yan kasarsa game da koma bayan jarin da ake zubawa a kasar. Yace Afirka ta kudu ba tana kan hanyar rushewa bane, kuma jam'iyar sa tana iya tafiyar da al'amuran kasar da ita ce tafi karfin tattalin arziki a Afirka, ko da shike masana suna shakkar hakan. Wannan ma shi ya sanya wakilai a zauren taron na ANC sukai ta yiwa Zuma shagube, lokacin da ya su hada hannu domin kawo karshen cin rashawa, saboda tun da ya kama mulki a shekara ta 2009 yake fama da matsalar zargin cin rashawa.

Cyril Ramaphosa ANC Südafrika

Sabon mataimakin shugaban ANC Cyril Ramaphosa

A game da zaben Cyril Ramaphosa kan mukamin mataimakin shugaban jam'iyar ta ANC, masanin democradiya Steven Friedman ya nunar da irin wahalolin da zai fuskanta nan gaba a dangantakarsa da kungiyoyin kwadago a kasar. To amma duk da haka wani mutum dake sharhi game dashi yace:

"Ramaphosa mutum ne dake da kima a idanun jama'a, wanda yan kasa suka amince da al'amuransa. Yana da farin jini matuka a tsakanin bakar fata masu matsakaicin karfi da kuma a tsakanin kafofin yada labarai. Saboda haka ne nake ganin nan gaba kadan zai kai ga mukamin mataimakin shugaban Afirka ta kudu, abin da zai bashi damar taka muhimmiyar rawa a al'amuran gwamnatin kasar. Abin da za'a jira a gani shi ko idan ya kai ga hakan, za'a sami gyara a al'amuran siyasar kasar."

Wani masanin na Afrika ta kudu, Hein Möllers yace mafi yawan yan Afrika ta kudu har yanzu basu kai ga cin gajiyar democradiya ba tukuna.

Sauti da bidiyo akan labarin