Jacob Zuma ya maida kudin gwamnati | NRS-Import | DW | 12.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Jacob Zuma ya maida kudin gwamnati

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi biyayya ga umarnin kotu na mayar da kudaden da ake zarginsa da dauka daga asusun gwamnati don gyaran gidansa.

Hukuma tara kudaden shiga a kasar Afirka ta Kudu, ta bayyana a ranar Litinin cewa shugaban kasar Jacob Zuma ya mai da kudaden da ake zarginsa da yin badakalar su wajen kawata gidansa na kashin kansa. Hukumar ta ce ta cimma nasarar samun kudaden ne a lalitar gwamnati biyo bayan zaman da wata babbar kotun kasar ta yi a watan Maris din shekara ta 2016 inda ta umarce shi da ya biya dukkanin kudaden da hukmar ta ke zarginsa da yin amfani da su ba bisa ka'ida ba.

An dai yi ta cece -kuce a kan makudan kudaden da shugaban ya kashe wajen sarrafa gidan nasa, to amma Zuma ya sha ikirarin cewa kawata gidan nasa na da nasaba da inganta tsaro. A watan Yuni da ya gabata ne dai hukumar ta kalubalanci shugaba Zuma a gaban kuliya da yin zamba da dukiyar kasa inda kotu ta umarce shi da ya biya kudi dalar Amirka miliyan 16. Wannan dai na daga cikin zarge-zargen da ya fara shafar harkokin gudanar da mulkin shugaba Jacob Zuma a kasar Afirka ta kudu.