Jabeur na son ba marada kunya a Wimbledon | Zamantakewa | DW | 27.06.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Jabeur na son ba marada kunya a Wimbledon

An fara gasar tennis ta Wimbledon ba tare da 'yan wasan Rasha ba da Belarus ba, yayin da a rukunin mata Ons Jabeur ta Tunisiya ta sha alwashin bai wa marada kunya.

A an fara gasar Wimbledon a birnin Landan ba tare da Daniil Medvedev dan wasan mafi shahara a duniya ba, sakamakon dakatar da 'yan wasan Rasha da Belarus da aka yi saboda mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine. Hakazalika ba za a dama da mai matsayi na biyu na tennis a duniya Alexander Zverev ba saboda ya samu rauni.A yanzu dai hankali a ya koma kan Novak Djokovic dan asalin Sabiya, duk da jadadda matsayinsa na kin yin allurar rigakafin Covid-19, lamain da zai hana shi shiga gasar US Open a watan Satumba mai zuwa.

 A rukunin mata kuwa, ana sa ran yin kare jini biri jini ganin yadda Iga Swiatek ta daya ta duniya a tennis ta hallara yayin da gwanar nan ta Amirka Serena Williams za ta dawo. A daya hannun kuma Ons Jabeur, 'yar Tunisiya, za ta iya zama 'yar Afirka ta farko da za ta yi iya yin nisa a gasar ta London. Dama Jabeur ta lashe gasar tennis ta Berlin, wacce ke zama ta uku a tarihinta. A yanzu haka ma dai  'yar Tuniyar ce ke rike da matsayi na uku a duniya. 

Mata 'yan wasan kwallon kafar Kamaru

Mata 'yan wasan kwallon kafar Kamaru

Mako daya kafin fara gasar kasashen Afirka ta mata a Maroko daga 2 zuwa 23 ga watan Yuli, 'yan matan Faransa sun yi wa na Indomitable Lionesses na Kamaru dukan kawo wuka ci 4-0 a wasan sa da zumunci. 'Yan Kamarun da ke matsayi na 54 a jeren karshe na Fifa, sun yi mafarkin samun nasara a kan na Faransa da ke a matsayi na uku a duniya. Amma tun a minti 31 da fara wasa ne aka fara gasa wa 'yan matan kamaru aya a hannu, sai kuma minti 37.

Bayan dawowa hutun rabi lokaci, 'yan wasan Kamaru da suka samu matsayi na uku a gasar Afirka ta karshe ba su yi nasarar rama wa kura aniyarta ba, maimakom haka ma dai, an sake shan su a mintinu na 57 da 62. Mako guda ne ya rage wa Imdomitables Lionness wajen gyara damarar tinkrara wasansu na farko da  za su yi da  Zambia a gasar AFCON a ranar Lahadi 3 ga watan Yuli.

A kasar Jamus, kungiyar Union Berlin ta rasa dan wasanta dan asalin Najeriya Taiwo Awoniyi wanda ya rattaba hannu a kungiyar Nottingham Forest ta Ingila wacce ta haura Premier Lig a karon farko cikin shekaru 23 da suka gabata. Hasali ma dan Najeriyan ya zama mafi tsada da Nottingham ta taba saya a tarihinta. Ya kasance wanda ya fi cin kwallo a Union Berlin a kakar wasa da ta kare, inda ya zira kwallaye 15. Sai dai a fannin tattalin arziki sayar da dan wasan na gaba ya zame wa Union Berlin ci gaba domin ta sayar da Awoniyi a kan kudi miliyan 20 na Euro.

Sadio Mane sabon dan wasan FC Bayern Muenchen.

Sadio Mane sabon dan wasan FC Bayern Muenchen.

Dan asalin Brazil da ke bugawa a Manchester City wato Gabrie Jesus ya amince zai buga wa Arsenal kwallo na tsawon shekaru biyar a kan kwantiragin pan miliyan 45m. Yayin da Jude Bellingham mai shekara 18 da ke buga wa Dortmund ya ke jan hankali Liverpool. Tuni ma jaridar the sun ta ruwaito cewa Liverpool na da tabbacin daukan dan kwallon da ke bugawa babbar kungiyar kwallon kafar Ingila. Ita ma Tottenham ta fara waiwayar dan kwallon RB Leipzig dan kasar Croatia Josko Gvardiol dan wasan baya don sanin farashinsa. 

A Bayern Munich kuwa, Dan kasar Senegal Sadio Mane mai shekaru 30 da ta soyo daga Liverpool ta Ingila, inda ya bayyana cewa zai goya lamba 17, maimakon 10 da ya saba wanda Leroy sane zai goya. Tuni ma Sadio Mané ya zama dan wasan da zai samu albashi mafi tsoka a Bundesliga, inda zai samu kudi kusan Euro miliyan 25 a duk shekara, bayan da Yaya-babba ta soyo shi a kan kudi miliyan 42 na Euro.

Jesse Rodriguez daya daga cikin gwarzayen 'yan wasan a tsakanin matasa a Amirka, ya ci gaba da rike kambunsa na WBC, bayan da ya doke Srisaket Sor Rungvisi na Thailand bayan da alkalin wasa ya tsayar da wasan a turmi na 8 a ranar Asabar a San Antonio da ke jihar Texas din Amirka.

Rodriguez mai shekaru 22 ya yi nasarar mamaye abokin karawarsa a tsawon fafatawar, duk da cewa ya girme shi da shekaru 13, inda ma a zagaye na 7 ya fara kwantar da shi a kasa warwas. A yanzu dai ba a doke dan dambe Jesse Rodriguez ko sau daya ba a fafatawar 16 da ya yi ciki har da guda 11 da ya yi nasara kafin karshen lokaci.

Sauti da bidiyo akan labarin