Izra′ila za ta ci gaba da kai hari a Gaza | Labarai | DW | 12.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Izra'ila za ta ci gaba da kai hari a Gaza

Izra'ila ta ce za ta ci gaba da kai hari a Gaza ta hanyar amfani da jiragen yaki: Lamarin da le kashe rayukan fararen Hula. Sannan kuma akwai yiwuwar kai farmaki ta kasa.

Izra'ila ta ci gaba da yin luguden wuta a Gaza a wannan Asabar inda rahotanni ke cewar an kai hari kan wani masallaci da ake zaton 'yan kungiyar nan ta Hamas sun adana makamai masu yawan gaske.

Mai magana da yawun sojin Izra'ila Moti Almoz ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewar Izra'ila za ta ci gaba da hare-haren da ta ke kaiwa Gaza da jiragen yaki nan da sa'o'i 24 da ke tafe kuma akwai yiwuwar nan gaba kadan sojin kasar za su kai farmaki ta kasa.

Yau Asabar dai ita ce rana ta biyar da Iza'ila ta shafe ta na kai hari Gaza, inda a hannu guda mayakan Hamas da ke yanki suma suke cigaba da maida martani kuma bisa ga rahotannin da muke samu yanzu haka yawan wadanda suka rasu sakamakon rikicin ya kai 122.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe