Izra′ila ta kashe Palesdinawa hudu a Gaza | Labarai | DW | 08.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Izra'ila ta kashe Palesdinawa hudu a Gaza

Tun a ranar Litinin ne Izra'ila ta ke hare-hare ta sama da ta kasa a ziri gaza, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane hudu ciki har da mata da yara kanana.

Palesdinawa hudu sun rasa rayukansu a lokacin da rundunar mayakan sama ta izra'ila ta kai hare-hare da jiragen sama na yaki a zirin gaza. Tun a jiye Litinin da maraice ne dai Izra'ila ta fara kai samame ta kasa inda ta lalata gidajen Palesdinawa da dama tare da jikata mutane 17 ciki har da mata da yara kanana.

Gwamnatin Izra'ila ta dauki wannan mataki ne domin mayar da martani dangane da hare-haren rokokin da kungiyar Hamas ta ke kai mata. Tuni dai kungiyar ta Hamas ta rufe makarantu da wasu wuraren shakatwa da ke kewayen zirin Gaza. Kana ta sha alwashin daukar fansa a kan Izra'ila.

Ita dai Izra'ila ta ce a shirya take ta dauki duk matakan da suka wajaba ciki har da mamaye zirin Gaza domin hana Palesdinawa kai mata har- hare da rokoki. Palesdinawa sun bayyana cewar hare hare 70 ne Izra'ila ta kai musu a kudancin zirin Gaza kadai.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman