Italiya ta lashe gasar zakarun Turai | Labarai | DW | 12.07.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya ta lashe gasar zakarun Turai

Kasar Italiya ta lashe kofin zakarun Turai wato EURO 2020, bayan da ta doke Ingila da ci 3-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Italiyar dai, ta yi nasarar lashe wasan ne bayan da ta doge takwararta ta Ingila a bugun 'daga kai sai mai tsaron raga' da ci 3-2 a wasan karshe wato final, da aka doka a filin wasa na Wembley da ke birnin London a gaban mafi yawan 'yan kallon da ke goyon bayan kungiyar kwallon kafar ta Ingila.

Kasar Birtaniya dai, bata taba samun nasara lashe wannan gasar ba kuma wannan shi ne karonta na farko da ta kai wasan karshe a gasar.