1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya: Rikicin siyasa da tattalin arziki

Gazali Abdou Tasawa
August 13, 2019

Tsohon Firamnistan Italiya Matteo Renzi ya yi kashedin cewa kasar na iya fuskantar karayar tattalin arziki idan aka kuskura aka shirya sabon zabe a kasar a watan Oktoba mai zuwa

https://p.dw.com/p/3Nqqg
Italien Wahl | Matteo Renzi (PD)
Hoto: Getty Images/AFP/A. Pizzoli

Tsohon Firamnistan Italiya Matteo Renzi ya yi kashedin cewa kasar na iya fuskantar karayar tattalin arziki idan aka kuskura aka shirya sabon zabe a watan Oktoba mai zuwa kamar yadda Matteo Salvini shugaban jam'iyyar masu kyamar baki ke bukata bayan ficewar shi daga gwamnatin kawance da Firaminista Giuseppe Conte.

Renzi wanda ya bayyana bukatar ganin an kafa gwamnatin kwararrun jami'ai mai zaman kanta a kasar ta Italiya, ya ce ya yi imanin hakan zai haddasa karin kudin harajin TVA a kasar da kaso 25 cikin dari kuma hakan zai jefa tattalin arzikin kasar ta Italiya a cikin mawuyacin hali musamman a daidai lokacin da rikicin kasuwanci tsakanin Amirka da Chaina ke kara kamari baya ga matsalolin da kamfanonin kera motoci ke fuskanta a kasar Jamus. 

A share dai dai majalisar dokokin kasar ta dage zaman da za ta yi domin tsayar da ranar muhawarar yankan kauna ga gwamnatin Conte da Salvini ya shigar a gabanta har ya zuwa ranar 20 ga wannan wata na Agusta 

Zuwa karshen watan Satumba ne dai kasar ta Italiya da ke zama a matsayin ta uku a karfin tattalin arziki a tsakanin kasashe masu amfani da kudin Euro da kuma ke fama da tarin bashi da komabayan tattalin arziki za ta gabatar da kasafin kudinta na shekara a gaban kungiyar Tarayyar Turai kamar sauran takwarorinta na tarayyar Turan.