Italiya na aikin gano gawarwaki a Teku | Labarai | DW | 07.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya na aikin gano gawarwaki a Teku

Italiya ta sanar da cewa ta samu nasarar gano barakuzan jirgin ruwan da ta hakikance shine wanda ya yi hadari a Teku cikin watan Afirilun da ya gabata.

Gawarwakin bakin hauren da suka mutu a Tekun Bahar Rum

Gawarwakin bakin hauren da suka mutu a Tekun Bahar Rum

Hadarin dai ya yi sandiyar hallaka mutane kusan 900 da suka taso daga Libiya a kokarinsu na shigowa nahiyar Turai. A ranar 18 ga watan na Afirilu ne hadarin da aka bayyana da mafi muni a Tekun na Bahar Rum ya afku, inda kawo yanzu aka samu nasarar gano gawarwaki 24 kacal daga cikin daruruwan mutanen da suka rasa rayukansu. Gano barakuzan jirgin da aka yi a can karkashin Tekun kimanin tazarar kilomita 84 zuwa kasar Libiya na sanya sabon fata na yiwuwar kara gano gawarwakin mutanen. An dai samu nasarar ceto mutane 28 daga cikin bakin hauren da ke cikin wannan jirgi wanda ke makare da bakin haure. Rahotanni na nuni da cewa akallah mutane 1,800 ne suka nutse a Tekun na Bahar Rum a wannan shekara ta 2015 da muke ciki, duk dai a kokarinsu na tsallakowa Turai da suke wa kallon "Tudun mun tsira".