Giorgia Meloni ta sha rantsuwar kama aiki
October 22, 2022Talla
Firaminista Meloni ta sha rantsuwar kama aiki ne a gaban shugaban kasar Sergio Mattarella a fadar Quirinal da ke da matukar tarihi a kasar.
Jam'iyyar Brothers of Italy da ke da nasaba da masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa a Italiya, sun samu nasarar kafa gwamnati a karon farko tun bayan yakin duniya na biyu.
Tuni sabuwar firaministar ta fitar da sunayen majalisar ministocinta da suka hada da mata 6, yayin da kasashen duniya tuni suka fara aike wa da sakon tayata murna.