Italiya: Adadin ′yan gudun hijira ya karu a 2016 | Labarai | DW | 30.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya: Adadin 'yan gudun hijira ya karu a 2016

A wannan shekara da ke bankwana ta 2016, kasar Italiya ta ce ta karbi 'yan gudun hijira da bakin haure da yawansu ya zarta 181.000 da suka iso kasar ta hanyar ruwa. Kuma adadin na iya karuwa cikin kwanaki biyu.

Hakan ya nunar da karuwar adadin da aka samu da kashi 18 cikin 100, idan aka kwatanta shi da na 2015. Daga cikin wannan adadi, fiye da 8000 sun iso kasar ta Italiya ne cikin wannan watan na Disamba, inda ake ganin adadin kan iya karuwa a tsakanin ranekun Asabar da Lahadi na karshen wannan shekara. A cikin watan Octoba da ya gabata, 'yan gudun hijira da bakin haure 27. 400 ne aka kidaya da suka iso kasar ta Italiya, adadin da ake ganin ya zarce na ko wane lokaci.

Rahoton ya nunar cewa, kashi daya cikin biyar na 'yan gudun hijiran sun fito ne daga Tarayyar Najeriya. Sannan kuma sauran kasashen da aka fi samun 'yan gudun hijiran su ne Erytreya, Guinea, Cote d'Ivoir da kuma kasar Gambiya.