ISWAP ta kai hari kan sojojin Najeriya | Labarai | DW | 13.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ISWAP ta kai hari kan sojojin Najeriya

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe sojoji da kuma fararen hula a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. Kasar dai na cewa ta ci karfin ta'addancin da ake fuskanta tsawon shekaru.

A Najeriya bayanan da ke fitowa daga yankin arewa maso gabashin kasar, sun ce wasu hare-haren da ake ganin na mayakan Boko Haram ne, sun salwantar da wasu sojoji gami da fararen hula a jihar Borno.

Hare-haren da suka auku a garin Gajiganna da yammacin Juma'ar da ta gabata, sun kashe fararen hula hudu da sojojin Najeriyar uku.

Ana dai dora alhakin lamarin ne kan kungiyar nan da ke kiran kanta ISWAP, wadda ta kai hari musamman kan sansanin soji da ke a yankin.

Tun da fari ma sai da mayakan na tarzoma suka, afka wa wani sansanin soji da ke kusa da kauyen Tungushe, kamar yadda shaidu suka tabbatar.

Garuruwan Gajiganna da Tungushe dai na fuskantar hare-hare daga wadannan mayaka.