1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ilawa uku sun amsa cewa su suka kashe matashin Bafalasdinen nan

July 7, 2014

Sai dai amsa aikata wannan kisan bai kwantar da hankula a yankin ba domin har yanzu ana ci gaba da kai wa juna farmaki tsakanin Isra'ila da Hamas.

https://p.dw.com/p/1CXmT
Israel ermordeter palästinensischer Jungen
Hoto: SAID KHATIB/AFP/Getty Images

A Isra'ila uku daga cikin 'yan kasar da ake zargi, sun amsa cewa su suka yi wa matashin Bafalasdinen nan kisan gilla. Rahotanni daga majiyoyin masu bincike sun ce an kona matashin ne dan shekaru 16, da ransa. Sai dai amsa aikata wannan kisan bai kwantar da hankula a yankin ba. Yanzu haka dai ana ci gaba da kai wa juna hari tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas mai mulki a Zirin Gaza. Kakakin gwamnatin Isra'ila Mark Regev cewa yayi.

"Muna daukar matakan kare mutanenmu ne. Muna kai farmaki kan 'yan ta'adda a Zirin Gaza, wadanda ke harba rokoki kanmu. Dole Hamas ta daina wannan."

Sai dai a nata bangaren Hamas ta ce harba rokokin ramuwar gayya ne ga kashe 'ya'yanta da Isra'ila ta yi, inji Sami Abu Zuhri kakakin Hamas.

"Kashe baradan Kassam su tara a cikin daren Litinin mummunan abu ne. Isra'ila na ci gaba da muguwar manufarta ta mamaye, ba ta son zaman lafiya. Muna jaddada 'yancin mutanenmu na nuna turjiya da wannan mamaye."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Pinado Abdu Waba