Isra′ila za ta kori baƙin haure | Labarai | DW | 31.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila za ta kori baƙin haure

Gwamnatin Isra'ila ta bayyana aniyarta ta aiwatar da shirinta na mayar da wasu baƙin haure na ƙasashen Afirka da ke zaune a ƙasar zuwa wata ƙasa ta gabashin Afirka.

A lokacin da ya zanta da manema labarai a kan wannan batu ministan cikin gidan isra'ila ya nunar da cewar a watan Oktoba ne za a fara tisa ƙeyar baƙin ba tare da bayyana ƙasar da za ta karɓe su ba. Kimanin baƙin haure dubu hamsin ne waɗanda galibinsu suka fito daga ƙasashen Sudan da sauran ƙasahe ke zauna a Isra'ila.

Gwamnatin Benjamin Netanyahu za ta bai wa duk wanda za a fitar daga ƙasar kimanin Euro dubu da ɗari biyar don su riƙe a hannunsu. Sai dai kuma ta yi barazanar ɗaukan matakan rashin sani da sabo daga bisani kan duk baƙin da za su ci gaba da zama a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

Mawallafi : Mouhamadou Awal Balarabe
Edita : Abdourahamane Hassane