Israila za ta gina sabbin gidaje | Labarai | DW | 09.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila za ta gina sabbin gidaje

Kudirin Israila na gina sabbin matsugunan Yahudawa a yankin Falasdinawa

default

Israila ta ce za ta cigaba da shirinta na gina wasu sabbin gidaje 1300 a yankunan larabawa da ta mamaye a gabashin birnin Kudus. Sanarwar ta ci karo da kalamai na baya bayan nan dake nuni da cewa Israilan za ta jinkirta gina sabbin matsugunan a gabashin kudus a wani mataki na wanzar da cigaban zaman lafiya da Falasdinawa. Hakan dai na faruwa ne cikin wani yanayi na tsaka mai wuya ga Firaministan Israilan Benjamin Netanyahu wanda a yanzu haka yake kasar Amirka domin tattaunawa akan hanyoyin farfado da shirin zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya. Wani mai magana da yawun gwamnatin Amirka ya baiyana matakin da cewa babban abin takaici ne da sosa rai.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita        : Umaru Aliyu