Isra’ila za ta ɗage kangiyar sama da na teku da take yi wa Lebanon. | Labarai | DW | 07.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra’ila za ta ɗage kangiyar sama da na teku da take yi wa Lebanon.

A wata sabuwa kuma, gwamnatin ƙasar Lebanon ta bukaci Majalisar Ɗinkin Duniya da ta bai wa gwamnatin Jamus umarnin tura jiragen ruwan yaƙinta zuwa gaɓar tekun bahar rum na ƙasar don aiwatad da yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cim ma da Isra’ila. Wani kakakin gwamnatin ƙasar, ya faɗa wa maneman labarai a birnin Beirut cewa, an miƙa bukatar ne a cikin wata takarda ga Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniyar Kofi Annan. Hakan kuwa, ya zo ne jim kaɗan bayan da Isra’ila ta ba da sanarwar cewa, za ta ɗage kangiyar sama da na ruwa da take yi wa Lebanon ɗin tun daga yau alhamis. Tun fara yaƙinta da ƙungiyar Hizbullahi ne dai Isra’ilan ta shiga yi wa Lebanon ɗin kangiyar.

A halin yanzu dai, jiragen ruwan yaƙin Girka da na Italiya ne za su dinga sintiri a gaɓar tekun Lebanon ɗin kafin isowar jiragen ruwan Jamus a cikin makwanni biyu masu zuwa.