1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra’ila ta yi wa tashoshin jiragen ruwan Lebanon kangiya.

July 13, 2006
https://p.dw.com/p/Buqd

A rikicin da ke ta ƙara tsananta a yankin Gabas Ta Tsakiya, Isra’ila ta ba da sanarwar tura jiragen ruwan yaƙinta a harabar ruwan ƙasar lebanon, don su yi wa duk tashoshin jiragen ruwan ƙasar kangiya. Wani kakakin gwamnatin ƙasar Bani Yahudun, ya ce Isra’ila ta ɗau wannan matakin ne, don hana abin da ya kira ’yan ta’adda yin amfani da tashoshin jiragen ruwan Lebanon ɗin, wajen jigilar takwarorinsu da kuma kai wa wasu ƙungiyoyin da ke zaune a Lebanon ɗin makamai.

Isra’ila, ta ba da sanarwar yin katsaladan a harabobin ruwan Lebanon ɗin ne, sa’o’i kaɗan bayan da jiragen saman yaƙinta suka kai hari a kan filin jirgin saman birnin Beirut yau da safen nan, abin da ya janyo rufe filin ma gaba ɗaya ga sufurin jiragen sama. Rahotannin da muka samu sun ce a wani harin jiragen saman yaƙin Isra’ila a kudancin Lebanon kuma, a ƙalla faraen hula 40 ne suka rasa rayukansu.