Isra′ila ta sako fursunonin Falasɗinu | Labarai | DW | 14.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila ta sako fursunonin Falasɗinu

Dubban Falasɗinawa na gudanar da shagulgula na nuna murna da farin ciki a fadar shugabn ƙasar a Ramallah da ke a Gaɓar kogin Jodan.

Jagoran Falasɗinawa wanda shi ne ya tarbesu a Ramallah Mahamud Abbas ya ce wannan wata rana ce ta farin ciki, sannan ya ƙara da cewar : Ya ce: '' Wannan kishi na farko kennan, kuma za mu ci gaba da yin gwagwarmaya har sai a sako dukkanin magoya baya mu da ake tsare da su.''

Isra'ila ta sako fursunoni 26 waɗanda ke cikin rukunin na fursuna 104 da za a sako a nan gaba. Yau da yamma aka shirya za a soma yin zagaye na biyu na tattaunawa sake farfaɗo da shirin zaman lafiya, tsakanin Yahudawan da Larabawan Falasɗinu bayan da shirin ya cije sama da watanni tara a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu