Isra′ila ta saki kuɗaɗen harajin Falasɗinu | Labarai | DW | 25.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila ta saki kuɗaɗen harajin Falasɗinu

Gwamnatin ta ba da izinin zuba kuɗaɗen harajin da ta ke cirewa ga al'ummar larabawa mazauna yankunan da ta mamaye zuwa ga hukumar Falasɗinawa.

A cikin wata sanarwa da ofishin fira ministan ta sanar, ta ce an yanke shawarar ne a ƙarshen wani taron majalisar ministocin. A cikin watan Disamba na shekarar bara ne, Isra'ila ta dakatar da shirin, bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da Falasɗinu a matsayin yar kallo a majalisar.

Sannan ta ummarci ministan kuɗi na ƙasar da ya zuba kuɗaɗen ga hukumar Falasɗinawan. Hakan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurika Barack Obama ya kammala wata ziyara a yankin gabas ta tsakiya. Masu yin sharhi a kan al'amura na ganin wannan mataki zai taimaka a samu ƙarin fahimtar juna tsakanin ƙasashen biyu.

Mawallafi : Abdourahamene Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh