1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kashe wasu kwamandojin Hamas

August 21, 2014

Rahotannin daga Gaza na cewar wasu jerin hare-hare da dakarun Izra'ila suka kai sun yi sanadiyyar rasuwa wasu kwamandojin Hamas guda uku.

https://p.dw.com/p/1CyVX
Raketenangriff auf Gaza Israel 20.08.2014
Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images

A wani sako da Hamas din ta fidda, ta ce mutanen da suka hada da Mohammed Abu Shammala da Raed al-Attar da kuma Mohammed Barhoum sun rasa ransu ne bayan da aka kai farmaki kan wani gini da suke ciki a kudancin Rafah.

Kisan wadannan kwamandojin dai na zuwa ne bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi tsakanin Hamas din da Isra'ila ta rushe, batun da ya sanya kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe cigaba da nuna damuwa dangane da yanayin da ake ciki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Ummaru Aliyu