Isra'ila ta kashe babban kwamandan Hamas na Lebanon
September 30, 2024Kungiyar Hamas ta Falasdinawa da ke yaki da Isra'ila a Gaza ta ce hare-haren Isra'ila a kudancin Lebanon da ke yankin Gabas ta Tsakiya sun halaka babban kwamnadanta Fateh Sherif Abu el-Amin, tare da wasu iyalansa. Sannan, akwai wasu kwamandoji uku wato Mohammad Abdel-Aal, da Imad Odeh da kuma Abdelrahman Abdel-Aal.
Karin bayani: Fargabar ta'azzarar rikici bayan kisan Nasrallah
Rundunar sojin Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da kai farmaki a Lebanon, har sai ta murkushe duk wani burbushi na kungiyar Hezbollah da aminiyarta Hamas ta Falasdinu, wadanda ke samun goyon bayan Iran. Dama ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya gana da firaministan Lebanon Najib Mikati a Beirut babban birnin kasar, inda ya yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da barin wuta a Lebanon nan take.