Isra'ila ta kai mummunan farmaki a Gaza
July 7, 2024Kungiyoyin bada agajin sun ce harin da Isra'ilar ta kai kan Asibitin Al-Aqsa a birnin Deir al-Balal ya yi sanadin rayuwakan mutum shida da kuma yara biyu. Ko a ranar Asabar ma'aikar kiwon lafiya ta Gaza da ke karkashin jagorancin kungiyar Hamas, ta ce wasu mutum 16 sun mutu sakamakon harin da aka kai kan wata makaranta da ke karkashin kulawar hukumar 'yan gudun hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, inda 'yan gudun hijira ke samun mafaka.
Karin bayani: Mali da Nijar da Burkina sun juya wa ECOWAS baya
Zafafa kai hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta ce za ta tura da tawagarta zuwa Doha domin ci gaba da tattaunawar sulhu. Sai dai kuma kakakin Firanministan Benjamin Netanyahu, ya ce zabi ya rage wa Hamas kan yadda za a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sakin wadanda take ci gaba da tsare su.