Isra′ila ta kai hari kan sojojin Siriya | Labarai | DW | 04.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila ta kai hari kan sojojin Siriya

Jiragen yakin Isra'ila sun kaddamarn da jerin hare-hare ta sama a wasu cibiyoyin sojin kasar Siriya da ke kudanci da kuma a yankin Arewa maso Gabas na kasar.

A yammacin ranar Litinin jiragen yakin Isra'ila sun kaddamar da jerin hare-hare ta sama a wasu cibiyoyin sojin kasar Siriya da ke a yankin Qouneitra na kudancin kasar.

Kamfannin dillancin labaran gwamnati na kasar ta Siriya wato Sana ya ruwaito wata majiyar sojin Siriyar na cewa wasu jiragen yaki masu saukar angulu na Isra'ila ne suka kaddamar da hare-haren da rokoki inda amma ya ce ba a samu asarar rayuka ba, sai ta kadarori.

Kazalika Isra'ilar ta kaddamar da wasu hare-haren makamai masu lizzami kan birnin Boukamal na Arewa maso gabashin kasar ta Siriya kusa da iyaka da Iraki.

Kuma a wani abun da ba ta saba yi ba, a wannan karo Isra'ilar ta fito fili ta dauki alhakin harin na birnin Qouneitra wanda ta ce martani ne ga yunkuri da wasu suka yi na dasa wasu bama bamai kirar gargajiya kan iyakarta da kasar ta Siriya.