Isra′ila ta hana ministocinta zuwa masallacin Al-Aqsa | Labarai | DW | 08.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila ta hana ministocinta zuwa masallacin Al-Aqsa

Firaministan Isra'ila ya bai wa hukumar 'yan sandar kasar umarnin hana ministocin gwamnatinsa zuwa masallacin Al-Aqsa Domin kontar da tarzomar falasdinawa.

Rahotanni daga kasar Isra'ila na cewa Firaministan kasar Benjamin Natanyahu ya bai wa hukumar 'yan sandar kasar izini na ta haramta wa ministocin gwamnatinsa damar shiga masallacin Al-Aqsa na birnin Kudus ko Jerusalem .

Jaridar kasar Isra'ila mai suna Haaretz wacce ta ruwaito labarin, ta ce shugaban gwamnatin kasar ta Isra'ila ya dauki wannan mataki ne a wani yinkuri na neman rage tsamar da ke da akwai tsakanin Isra'ila da kasar Jodan dama kuma neman kashe wutar tarzomar da Falasdinawa ke yi yau da 'yan kwanaki.

Ziyartar masallacin Al'aqsa da wasu ministoci ko 'yan majalissar dokokin kasar ta Isra'ila ke kaiwa a wasu lokutta na kasancewa ummulhaba'isan tarzomar da Falasdinawa ke tadawa. Masallacin Al-Aqsa dai guri ne wanda mabiya addinan biyu na Muslunci da addini Yahudu ko wane ke ikrarin kasancewa tsarkakakken gurin ibada na addininsa.