Israi′la ta dauki alhakin kashe Abu Jihad | Labarai | DW | 02.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israi'la ta dauki alhakin kashe Abu Jihad

Bayan kawaici na shekaru 25 Isra'ila ta fito da bayani game da mutuwar Abu Jihad, tsohon mataimakin shugaban kungiyar PLO mai fafutukar 'yantar da yankin Falisdinawa.

Ta ce tsohon mataimakin na Yassir Arafat an kashe shi ne a kasar Tunisiya a shekarar 1988. Hakan ya bayyana ce a cikin firar da rundunar sojin Isra'ila ta yarda aka daita wadda a yayinta wasu sojoji na musamman suka dauki alhakin kashe Abu Jihad, wanda sunansa na yanka shi ne Khalil al Wasir. Rundunar sojin ta ce daga cikin wadanda suka aikata wannan kisan akwai mutane biyu da ke tare da gwamnati mai ci yanzu. Wadannan kuwa sune ministan tsaro Ehud Barak , wanda a wancan lokaci ya shugabancin dakarun sojin kasar da kuma mataimakin firaiminsta, Mosche Jaalan. To sai dai su biyu nan sun ki sun ce uffan game da wannan rahoto.

Shi dai Abu Jihad an zarge shi ne da laifin kai munanan hare hare da suka hada da wanda aka kai akan wani bus a shekarar 1978 da Yahudawa 38 suka rasa rayukansu a cikinsa. A karshen shekarar 1987 ne dai Falisdinawa suka ta da kayar baya a yankunansu da Isra'ila ta mamaye.

Mawalafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal