Isra′ila ta ci gaba da shirinta na yi wa Falisdinawa mamaya | Labarai | DW | 19.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila ta ci gaba da shirinta na yi wa Falisdinawa mamaya

Ana ci gaba da la'antar Isra'ila bisa manufarta ta yi wa Falisdinawa mamaya

Isra'ila ta sha suka game da shirinta na gina gidaje 1500 a arewacin birnin Kudus. Kamfanin dillacin labarun Falisdinawa Ma'an ya rawaito cewa shugaban Falisdinawa, Mahmoud Abbas zai shigar da kara a komitin sulhu na Majalisar Dinkin duniya Duniya. Kungiyar Tarayyar Turai ita kuma ta yi kakkausan suka ga shirin gina sabbin matsugunan. Helkwatar kungiyar da ke birnin Brrussels na kasar Beljiyam ya ce mamayar da Isra'ila ke wa yankunan Falisdinawa ta saba wa dokokin kasa da kasa, tana kuma yin ciikas ga kokarin samar da zaman lafiya. Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ita kuma ta yi magana game da matakai na gaban kai da Isra'ila da Falisdinawa ke dauka.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru-Dan Ladi Aliyu