Isra’ila ta ce za ta dakatad da kai hare-hare a kudancin Lebanon har tsawon sa’o’i 24. | Labarai | DW | 31.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra’ila ta ce za ta dakatad da kai hare-hare a kudancin Lebanon har tsawon sa’o’i 24.

Mazuna ƙauyukan kudancin Lebanon, sun fara ƙaurace wa matsugunansu tun safiyar yau, bayan da Isra’ila ta ba da sanarwar cewa ta amince ta tsagaita buɗe wa yankin wuta har tsawon sa’o’i 24, don bai wa mazauna damar tserewa daga filin dagar. A lokaci ɗaya kuma, jami’an ceto na ta ƙoƙarin kai taimako ga ƙauyukan da bamabaman Isra’ilan suka fi ragargazawa. Rahotannin sun ce wannan matakin da Isra’ilan ta ɗauka, ya biyo bayan angaza wa gwmantain ƙasar da sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleeza Rice ta yi ne, yayin ziyararta a birnin Ƙudus. Wasu rahotannin da suka iso mana daga birnin Beirut kuma, sun ce wani ayarin motocin jami’an ba da taimakon agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya tashi daga birnin Beirut zuwa garin Tyre da ƙauyen Qana, inda hare-haren bamabaman da jiragen saman yaƙin Isra’ila suka jiya, suka halakad da fararen hula fiye da 60 a lokaci ɗaya.